Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance
 

Ankararwa Kan Sirri

Ankararwa Kan Sirri

Mun gode da kuka yarda ku shiga shirin Lada Don Adalci. Mun duƙufa wajen kare bayananku da kuma haƙƙinku na a tsare bayananku.

Wannan ankararwar na bayyana yadda za mu iya yin amfani da bayananku idan kuka:

Cikin wannan ankararwar kan adana sirri, idan muka ce:

  • “Dandalin Yanar Gizo,” muna nufin kowane shafi mallakarmu da ke haɗe da ko kuma yake magana a kan wannan ankarawar
  • “Ayyuka,” muna nufin shafin dandalin yanar gizonmu, da sauran ayyuuka da suka haɗa da talla da wasu taruka

Manufar wannan ankararwar ita ce don mu yi muku bayani ƙarara daidai gwargwado kan bayanan da muke karɓa, da yadda muke amfani da su, da kuma haƙƙin da kuke da shi game da su. Idan akwai wani sharaɗi da ba ku amince da shi ba a wannan ankararwar kan adana sirri, muna roƙonku da ku dakatar da amfani da kayayyakinmu nan take.

Muna roƙon ku ku karanta wannan bayanin bisa ankarawa kan sirri cikin natsuwa, saboda zai taimaka muku wajen fahimtar abin da muke yi da bayananku da muke karɓa.

Bayanan da Ake Karɓa Kai-Tsaye

A taƙaice: Wasu bayanan – kamar adireshinku na intanet (IP address) da/ko siffar na’urarku – ana karɓar su kai-tsaye idan kuka ziyarci shafinmu na intanet.

Muna karɓar wasu bayanai kai-tsaye idan kuka ziyarci shafin, ko kuka yi amfani da shi, ko kuma kuka zagaya a ciki. Waɗannan bayanan ba sa nuna wasu abubuwa na musamman game da ku (kamar suna ko hanyar tuntuɓa), amma za su iya ƙunsar siffar na’urarku kamar adireshin IP, da na manhajar shiga intenet (browser), da samfurin tsarin kwamfutarku (operating system), da harshen da kuka zaɓa, da adireshi-adireshin da kuka aika, da sunan na’ura, da ƙasa, da wurin da kuke, da kuma bayani kan lokaci da yadda kuke amfani da shafinmu, da sauran bayanai. Ana buƙatar waɗannan bayanan ne kawai don tsaro da kuma ayyukan shafinmu, da kuma ƙididdiga da muke yi da haɗa rahotanni.

Kamar sauran harkoki, muna kuma karɓar bayanai ta hanyar cookies da fasahohi irinsa.

Bayanan da muke karɓa sun ƙunshi:

  • Bayanan Amfani da Gudanarwa: Bayanan amfani da gudanarwa na da alaƙa da yin amfani da gano matsala da kuma yadda na’urorinmu ke karɓar bayanai kai-tsaye idan kuka shiga shafinmu, wanda kuma muke ajiyewa rumbunmu. Ya danganta da yadda kuke mu’amala da mu, bayanan wannan rumbun za su iya ƙunsar adireshin IP, da bayanan na’ura, da nau’in manhajar shiga intanet (browser) da kuma ayyukanku a shafin (kamar rana da lokacin amfani da shafin, da shafuka da kuma fayil-fayil da kuka duba, abubuwan da kuka nemi ƙarin bayani akan su da sauran abubuwan da kuka yi kamar nau’in abin da kuka yi amfani da shi), bayanan abin da na’urarku ta aiwatar (kamar ayyukanta, da miƙa rahotannin kuskure (wani zubin ana kiran su ‘saƙonnin hatsari’ ko ‘crash dumps’da turanci) da kuma saiti na’urar).
  • Bayanan Na’ura: Muna karɓar bayanan na’ura kamar na kwamfutarku, da waya, da babbar waya (tablet), da sauran na’urorin da kuke amfani da su wajen shiga shafin. Ya danganta da na’urar da kuke amfani da ita, bayanan na’urar za su iya ƙunsar adireshin IP (ko layin proxy) lambobin da ke fayyace manhaja, da wuri, da nau’in manhajar shiga intanet (browser), da samfurin kayan aiki, da kamfanin da ke samar da layin intanet, da kuma sunan kamfanin da ya ƙera wayarku, da samfurin kwamfuta, da bayanan tsarin na’ura.
  • Bayanan Wurin da ake: Muna karɓar bayanan wuri, kamar bayanan inda na’urar da kuke amfani da ita take, wanda ka iya yin daidai ko akasin haka. Yawan bayanan da muke tatsa ya danganta da nau’in na’urar da kuke amfani da ita wajen shiga shafin da kuma tsarinta. Misali, za mu iya yin amfani da fasahar GPS da sauran fasahohi don karɓi bayanin wurin da kuke (ta hanyar amfani da adireshin IP naku). Za ku iya hana mu karɓar waɗannan bayanan ta hanyar dakatar da mu daga samun su ko kuma ku kashe maɓallin gane wurin da kuke (location settings) a kan na’urarku. Sai dai kuma a kula, idan kuka zaɓi ku hana mu bayanan ba lallai ne ku iya amfani da wasu kayayyakin ba.

Ta Yaya Muke Amfani da Bayananku?

Muna amfani da bayanan da muka karɓa don gudanar da wasu harkokin kasuwanci daban-daban kamar haka. 

Za mu iya yin amfani da bayananku wajen gudanar da abubuwa kamar haka:

  • Don kare ayyukanmu. Za mu iya yin amfani da bayananku wajen yunƙurinmu na kare shafinmu da ba shi tsaro (misali, don bin diddigin zamba da yin rigakafi.)
  • Don tabbatar da bin ƙa’idojinmu, da sharuɗa, da tsare-tsare wajen bin dokoki da kuma bin umarnin hukumomi.
  • Don kammala da kuma taimaka wa ayyukan da ake cikin gudanarwa
  • Don jagorantar da kuma kula da shafin
  • Don gudanar da bincike da samar da ci gaba
  • Don gudanar da binciken-binciken da hukuma ta amince da shi

Ko Muna Amfani da Cookies da Sauran Fasahohin Bin Diddigi?

A Taƙaice: Za mu iya amfani da cookies da sauran fasahohin bin diddigi (kamar web beacons da pixels) don karɓa ko ajiye bayanai.

Cookies da sauran fasahohi irinsa za su iya taimaka mana wajen gane ku kai-tsaye idan kuka sak dawowa shafinmu ko kuma manhaja. Cookies kan taimaka mana wajen tantance yadda ake tururuwa a shafin, da inganta shafin da kuma yin hasashen wadanne kayayyaki ne aka fi so. Za kuma mu iya yin amfani da waɗannan bayanai wajen tallata wasu kayayyaki na musamman ga masu amfani da su, waɗanda alamu suka nuna sun fi sha’awar sha’awar wani ɓangare.

An tsara akasarin manhajojin shiga intanet don su amince da cookies kai-tsaye. Idan kuka dama, za ku iya tsara manhajarku ta shiga intanet ta goge ko kuma ta yi watsi da cookies. Idan kuka zaɓi ku yi watsi da cookies, hakan zai iya shafar wasu ɓangarori ko ayyukan shafinmu.

Ta Yaya Muke Tsare Bayananku?

A Taƙaice: Muna da zimmar kare bayananku ta hanyar tsarawa da kuma ɗaukar matakan tsaro.

Mun aiwatar da tsari na aikace da kuma na tsararrun matakan tsaro don kare duk wasu bayanai da muke amfani da su. Sai dai kuma, duk ƙoƙarinmu na kare bayananku, babu wani da aka ɗora a intanet da zai samu tsaro 100 bisa 100, saboda haka ba za mu iya ba da tabbaci ba cewa masu kutse ko miyagun intanet ko wasu da ba a saka su ba ba za su iya karya tsaronmu ba kuma su saci bayanai ko kuma su sauya bayanan. Duk da cewa za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu game da bayananku, ku saka bayanan naku na musamman a shafinmu kuna masu sanin cewa akwai haɗari. Ya kamata ku shiga shafin a wurin da ke da tsaro kaɗai.

Matakai Kan Harkokin Kada-a-Bi-Diddigi

Akasarin manhajojin shiga intanet da kuma tsarin wasu wayoyi da manhajojinsu na da tsarin Kada-a-Bi-Diddigi wato Do-No-Track (“DNT”) ko saiti da za ku iya sakawa don nuna abin da kuka fi so game da adana sirrinku cewa kada a bi diddigin ayyukan da kuke yi intanet da karɓar bayanan. A wannan matakin ba a tsayar da wani tsarin bin diddigi (DNT) takamaimai da za a yi amfani da shi ba. Saboda haka, a yanzu ba ma amsa zaɓin da kuka yi game da DNT ko kuma wani tsari da ke bayyana mana buƙatarku ta cewa kada a bi diddigin ayyukanku. Idan mun yanke shawarar wani tsari da za mu bi nan gaba wajen bin diddigi, za mu sanar da ku hakan a wannan ƙunshin bayanan game da adana sirri da za mu sabunta.

Sanarwa Ga Mutanen da Ke Shiga Wannan Shafin Dadalin Yanar Gizon Daga Wajen Amurka

Muna iko tare da kula da ayyukanmu ne daga Amurka, mazauna Amurka ne ke iya samun su, sannan kuma babu wata dokar wata jiha da ke kanmu, ko ƙasa, ko yanki, sai ta Amurka kawai. Za a iya amfani da kuma ajiye da duk wani bayani da kuka bayar ta hanyar amfani da kayayyaki, ko aika shi tare da samun sa a cikin Amurka da wasu ƙasashe, waɗanda ba lallai su ba da tsaro yadda ya kamata ba kan bayaananku irin na ƙasar da kuke zaune. Idan ba kwa so bayanan rayuwarku su bar ƙasarku, muna roƙonku da kada ku ba wa Lada Don Adalci kuma kada ku yi amfani da shafinmu na intanet. Da zarar kun ba wa Lada Don Adalci bayanan rayuwarku, kenan kun amince ƙwarai da gaske cewa za a iya kai bayanan naku Amurka.

Shirin Lada Don Adalci ko kuma masu yi masa wasu ayyuka ka iya aika bayanan rayuwarku daga Da’irar Tattalin Arziki ta Turai wato European Economic Area (EEA) zuwa wasu ƙaasashe, waɗanda har yanzu Hukumar Turai ba ta amince cewa wasu daga ciki za su iya samar da cikakken tsaro ba kan bayanan yadda zai dace da tsarin EEA. Idan a tura zuwa ƙasashen da ba sa buƙatar tsari kamar na EEA, Lada Don Adalci na amfani da tsare-taren shari’a don kare bayanan rayuwarku, ciki har da dokokin ƙulla yarjejeniya da kuma tabbaci a rubuce daga kamfanonin da ke samar da layi.

Za mu kiyaye bayanan rayuwarku bisa wannan Tsarin Adana Sirrin ba tare da lura da inda aka ajiye su ba ko kuma amfani da su.

Adireshi Zuwa Wasu Shafukan

Adireshin da danganewa ga wasu shafukan intanet ɗin da ba na Gwamnatin Amurka ba ko kuma yin kasuwanci, ko wani kamfani, ko sunayen hukumomi da ke kan shafin Lada Don Adalci, an tsara su ne don sauƙaƙa wa masu amfani da shafin. Amfani da su ba ya nufin amincewa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ko shirin Lada Don Adalci.

Dokar Zamba ta Intanet

An haramta duk wani yunƙurin saka bayanai ko sauya su ba bisa ƙa’ida ba a kan wannan shafin kuma za a hukunta mutum a ƙarƙashin Dokar Zamba ta Intanet ta 1986 wato Computer Fraud and Abuse Act of 1986, 18 U.S.C.§ 1030, da kuma sashe na 1001 na Title 18.

Tsarin Ankarawa kan Sirri na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka

Za ku iya ganin tsarin ankarawa kan sirri na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a: https://www.state.gov/privacy-policy/

Yadda Za Ku Tuntuɓe Mu

Idan kuna da tambayoyi game da tsarinmu na ankarawa kan sirrin ko amfani da bayanai muna maraba da tsokaci. Za a iya samun kundin bin dokokin tsarin adana sirri a Privacy Impact Assessments (PIA) da and Systems of Records Notices (SORN). Don samun ƙarin bayani game da Tsarinnmu na Ankarawa kan Sirri, muna roƙonku da ku tuntuɓe mu a privacy@state.gov ko kuma a aiko mana imel a:

Office of Global Information Services
Privacy Office – A/GIS/PRV
State Annex 9
U.S. Department of State
Washington, DC 20006

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Please visit our Tor-based tips-reporting channel at: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Signal don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Telegram don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Ku duba shafin da zai ba ku ƙarin bayani game da turo rahoto a: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Skip to content