An kafa Ƙungiyar Abu Nidal (Abu Nidal Organization –ANO) a 1974 bayan ta balle daga kungiyar Palestinian Liberation Organization. ANO tana biɗan ta kawar da Isra’ila daga ban kasa sannan ta dinga koƙarin hana aiwatar da shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Kungiyar ta dauki alhakin kai hare-hare da dama, ciki har da harin bam kan jirgin sama na TWA Flight 840 (hyperlink) da garkuwa da jirgin sama na Pan Am Flight 73.
A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ANO a matsayin kungiyar ta’addanci ta kasar waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO) bisa sashe na 219 na Dokar Kaura da kuma Zama Dan Kasa da aka yi wa kwaskwarima. Ranar 1 ga Yunin 2017, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta cire ANO daga matsayin FTO.