Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance

Daular Islama ta Iraqi da Syria a Yankin Sahara ko ISIS A Babban Yankin Sahara (ISIS in the Greater Sahara –ISIS-GS)

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Ba da gudunmawarka.

An kafa Daular Islama ta Iraqi da Syria a Yankin Sahara ko ISIS A Babban Yankin Sahara (ISIS in the Greater Sahara –ISIS-GS) a 2015 bayan ta ɓalle daga al-Mourabitoun, wadda ta ɓalle daga al-Qa’ida, kuma ta yi mubaya’a ga ISIS. Ƙungiyar da asalinta shi ne Mali da kuma gudanar da ayyukanta a kan iyakar Mali da Nijar, tana kuma yin ayyuka a Burkina Faso.  (ISIS-GS) ta ɗauki alhakin kai hare-hare da dama, ciki akwai na ranar 4 ga Oktoban 2017 kan wani sintiri na haɗin gwiwa tsakanin Nijar da Amurka a yankin Tongo Tongo da ke Nijar, wanda ya jawo kisan sojan Amurka huɗu da na Nijar huɗu. A Nuwamban 2019,  ISIS-GS ta kai hari kan sansanin sojan Mali da ya kashe sojoji 54.

A ranar 23 ga Mayun 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-GS a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima.   Kafin haka, a ranar 16 ga watan Mayun 2018 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-GS matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana ISIS-GS taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da  ISIS-GS.  Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa ISIS-GS kayan aiki da gangan.

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Please visit our Tor-based tips-reporting channel at: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Signal don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Telegram don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Ku duba shafin da zai ba ku ƙarin bayani game da turo rahoto a: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Skip to content